Majalisar wakilan Najeriya ta amince da kasafin kudin 2013

tambuwal
Image caption Shugaban Majalisar wakilai, Aminu Waziri Tambuwal

A Najeriya, majalisar wakilai ta kasar ta zartar da kudirin dokar kasafin kudin badi wanda ya baiwa gwamnatin tarayya damar kashe Naira tirilayan biyar.

Majalisar ta zartar da kasafin ne kan hasashen cewa za'a sayar da gangar mai akan dala saba'in da tara sabanin hasashen bangaren zartarwa na dala saba'in da biyar.

Haka kuma majalisar ta amince da sabon kasafin kudin ne bisa sharadin cewa bangaren zartarwa zai cigaba da aiwatar da tanade-tanaden kasafin kudin bana a shekarar ta badi.

Manazarta na ganin cewar amincewa da kasafin kudin, baya wani tasiri a kan rayuwar akasarin al'ummar kasar.

A 'yan shekarunan dai, Najeriyar bata iya aiwatar da daukacin kasafin kudinta na shekara abinda kuma kan jawo koma baya ga tattalin arzikin kasar.

Karin bayani