Jirgin ruwa ya kife da mutane 55 a Somaliya

Jirage a gabar Somalia
Image caption Jirage a gabar Somalia

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana fargabar 'yan kasar Somaliya da Habasha 55 ne suka rasa rayukansu bayan da jirgin ruwansu ya kife a gabar ruwan Somaliya.

Majalisar ta ce jirgin, wanda ke dauke da mutane fiye da kima ya shiga matsala bayan barin tashar ruwa ta Bossasso a arewa maso gabashin Somaliyan.

Jirgin na kan hanyarsa ne ta zuwa Yemen.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan shi ne hadarin da yafi cin rayukan mutane a kan tekun Aden tun watan Fabrairun bara lokacin da wasu 'yan cirani 'yan Somaliya 57 suka nutse.

Kowace shekara dai dubban mutane daga kusurwar Afurka kan tsallaka teku domin gujewa rikice-rikice da matsanancin halin rayuwa da dai sauran matsalaoli.