An kwantar da ministan Syria a asibiti

Image caption Shugaba Bashar Al-Assad na Syria lokacin da yake rantsarda sabon ministan Tsaro.

An kwantar da ministan harkokin cikin gida na Syria Mohammad Shaar a wani asibiti da ke kasar Lebanon, bayan ya samu raunuka a cikin wani harin bam a birnin Damascus makon da ya gabata.

Ba a bayyana irin raunukan da ya samu ba, amma kuma ana kyautata zaton ba su yi tsanani ba.

Haka nan ba a bayyana dalilin da ya sa aka fitar da shi daga kasar ba alhalin asibitoci na aiki a birnin Damascus.

Wakilin BBC ya ce, an tsaurara matakan tsaro a kewayen asibitin da aka kai ministan bayan da ya sauka a filin jirgin sama na Beruit.

Rahotanni na cewa ko dai ya ji rauni ne a cikinsa, ko a kafada, ko kuma a bayansa.

Karin bayani