An yi bata kashi a birnin Iskandariya na Masar

matasa
Image caption Matasa sun fafata a Masar saboda bambamcin ra'ayi

An yi bata kashi tsakanin kungiyar 'yan uwa musulmi da kuma masu adawa da su, a gaban wani masallaci a birnin Iskandariya na Masar,kwana daya kafin a fara zaben raba gardama a karo na biyu a kan kudin tsarin mulkin kasar.

Jami'an tsaro sun harba barkonon tsohuwa domin raba bangarorin biyu.

Ko a makon daya gabata ma, saida aka samu tashin hankali a gaban wannan masallacin.

'Yan adawa a Masar dai na ganin gyaran da za'a yiwa kudin tsarin mulkin ya baiwa kungiyar 'yan uwa musulmi fifiko.

Karin bayani