Lockerbie: Libya za ta bude sabon bincike

Image caption Abdulbasit Al-megrahi wanda ake samu da laifi saka bam a jirgin ya jima yana fama da rashin lafiya kafin rasuwar sa,

Sabuwar gwamnatin Libya ta nuna cewa a shirye ta ke ta sake kaddamar da bincike a kan bam din da aka dasa a wani jirgin saman Amurka shekaru ashirin da hudu da suka gabata.

Jirgin dai ya fado ne a garin Lockerbie na Scotland sakamakon tashin bam din abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane dari biyu da saba'in a ranar 21 ga watan Disamba na shekarar 1988.

Jakadan Libya a Burtaniya, Mahmud Nacua ya shaidawa BBC cewa Libya a shirye ta ke domin taimakawa wannan lamarin,duk da ya ce za a dauki shekara guda kafin Tripoli ta samar da bayanan da ta ke da su.

Mutum daya ne kadai dan Libya aka tuhuma da hannu a tashin bam din, wato Abdulbasid al-Megarahi wanda ya rasu a watan Mayu na wannan shekara.

Karin bayani