An harbo jirgin majalisar dinkin duniya a Sudan ta kudu

Sojin majalisar dinkin duniya a Sudan
Image caption An harbo jirgi a Jahar Jonglei

Majalisar Dinkin Dunyiya ta ce an harbo daya daga cikin jiragenta masu saukar angulu a kasar Sudan ta kudu.

Wani mai magana da yawun Majalisar ya ce sojojin Sudan ta kudu ne suka harbo jirgin, kuma duk mutane hudu da suke ciki sun mutu.

Jirgin dai na kan hanyar sa ne ta zuwa jahar Jonglei

An dai kirkiro da aikin kiyaye zaman lafiyar majalisar dinkin duniyar a sudan ta kudu bayan da sudan ta kudun ta samu 'yancin kai daga Sudan a watan Yulin shekarar bara