'Yan adawar Masar sun soki zabe

Zaben raba gardama a Masar
Image caption 'Yan adawa sun soki zaben raba gardama

'Yan adawa a Masar sun yi kira da a gudanar da bincike game da zarge zargen tafka magudi a zabe, a kuri'ar jin ra'ayoyin jama'ar da aka gudanar kan sabon daftarin tsarin mulki mai cike da takaddama.

Korafin 'yan adawar sun hada da rashin bude wasu rumfunan zaben a kan lokaci, da kuma zargin cewa masu ra'ayin Islama sunyi ta kokarin rarrashin mutane su kada kuri'ar amincewa da daftarin tsarin mulkin.

Babu dai alamun kuri'ar amincewar da akai ta kadawa zata kawo karshen rikicin siyasar da ake ciki yanzu haka a kasar, illa iyaka ta sake bayyana irin girman rabuwar kawunan da aka samu a cikin Kasar

Sakamakon farko wanda bana hukuma ba, na nuni da cewa mafi akasarin 'yan kasar sun kada kuriar su ta amincewa da daftarin tsarin mulkin wanda yasa kasar ta rabu gida biyu.

Idan har aka amince da tsarin mulkin daga karshe , za a gudanar da zabukan 'yan majalisun dokoki nan da wasu watani biyu masu zuwa

Karin bayani