An kai harin kunar bakin wake a Kano

'Yan sandan Najeriya
Image caption An kai wasu hare hare a Kano

Wasu 'yan kunar bakin wake sun kai hari kan kamfanonin sadarwa na wayar salula guda biyu a Kano dake arewacin Najeria.

Jami'an tsaro sun shaidawa BBC cewa wani dan kunar bakin wake ya kutsa kai da motarsa cikin ofishin kamfanin sadarwa na Airtel dake dandalin Malam Kato, inda ya jikkata mutum daya.

Haka kuma an kai wani harin ofishin wayar salula ta MTN a unguwar Bompai.

Duka 'yan kunar bakin waken dai sun rasa rayukansu.

Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai hare-haren guda biyu.

A baya dai kungiyar masu kaifin kishin Islama ta Boko Haram sun sha kai hari kan kamfanonin sadarwa na Salula a arewacin Najeriya, su na masu cewa su ke taimakawa jami'an tsaro su na kama mambobinsu.

Karin bayani