Za'a gudanar da zagaye na biyu na zaben raba gardama a kasar Masar

 Zaben raba gardama a kasar Masar
Image caption Zaben raba gardama a kasar Masar

A yau asabar ne za'a gudanar da zagaye na biyu na zaben raba gardama akan kundin tsarin mulki a kasar Masar.

Fiye da jami'an tsaro dubu dari biyu ne da suka hada da 'yan sanda da sojoji aka tura sassa daban daban na kasar don tabbatar da tsaro.

Sai dai 'yan adawa sun yi korafin cewa an tafka magudi a zagayen farko na zaben.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu rikici a birnin Iskandiriya a juma'ar da ta gabata tsakanin masu kishin islama da kuma 'yan adawa a gaban daya daga cikin manyan masallatan birnin.

Wasu masu sharhi akan al'amura dai sun yi hasashen cewa akasarin yankunan da za'a gudanar da zagaye na biyu na zaben zasu kada kuri'ar amincewa ne da sabon kundin tsarin mulkin, kasancewar Jam'iyar 'yan uwa musulmi nada dimbin magoya baya a yankunan.

Matukar aka amince da sabon kundin tsarin mulkin dai, ana saran gudanar da zaben Majalisun dokoki ne a farkon shekara mai zuwa, sai dai kafin zuwan lokacin, ikon kafa dokoki zai ci gaba da kasancewa ne a hannun shugaba Morsi.

Kawo yanzu dai ba'a tantace irin matakan da 'yan adawa zasu dauka ba bayan an sanar da sakamakon zaben musamman idan akasarin al'ummomin kasar suka amince da sabon kundin tsarin mulkin.

Sai dai wasu da dama na fargabar cewa duk yadda sakamakon zaben ya kasance, za'a ci gaba da samun rarrabuwar kawuna tsakanin al'ummomin kasar.