Ana zaben raba gardama na karshe a Masar

Zabe a Masar
Image caption Daftarin tsarin mulkin Masar ya janyo cece kuce

A Kasar Masar ana can ana gudanar da kashi na biyu kuma na karshe na zaben jin ra'ayoyin jama'a kan kundin tsarin mulki da ake ta takaddama akansa.

Sakamakon da ba na hukuma ba na kuri'ar da aka kada a makon jiya a jahohi goma, ya nuna cewa kashi hamsin da bakwai cikin dari na mutanen da su ka kada kuri'unsu sun amince da kundin tsarin mulkin.

Sai dai kuma 'yan adawa sun yi korafin cewa an tafka magudi a zaben.

Ana kada kuri'ar ta yau ce a lardina goma sha bakwai kuma sune wuraren da ake ganin yawanci su na goyan bayan jam'iyyar 'yan uwa musulmi da kuma Shugaba Morsi wanda ya taimaka aka rubuta kundin tsarin mulkin.

An dai tsaurara matakan tsaro a inda ake yin zabukan

Karin bayani