Ana tattara sakamakon zaben raba gardama a Masar

Kidayar kuri'u a zaben kasar Masar
Image caption Kidayar kuri'u a zaben kasar Masar

A kasar Masar, yanzu haka ana can ana tattara sakamakon zaben kuri'ar raba gardama game da sabon kundin tsarin mulkin kasar.

A zagaye na biyu na zaben da aka gudanar jiya asabar a larduna goma sha bakwai, fiye da kashi saba'in cikin dari na mutanen kasar ne su ka kada kuri'ar su.

Wannan dai na daga cikin dalilan da yasa masu lura da al'amura ke ganin jama'ar kasar zasu amince da sabon kundin tsarin mulkin.

Jam'iyar 'yan uwa musulmi ta bayyana cewa sakamakon zaben wasu rumfuna da aka kidaya, sun nuna cewa akasarin wadanda suka kada kuri'a sun amince da kundin tsarin mulkin.

A bangare guda kuma an samu korafe korafen tafka magudi a zaben da suka hada da zargin kai kayayyaki a makare a wasu rumfunan zaben, da kuma zargin cewa 'ya'yan jam'iyar 'yan uwa musulmi na ta kokarin sa jama'a kada kuri'ar amincewa da kundin tsarin mulkin.

Sai dai duk da haka, 'yan adawa sun shiga cikin zaben kuma matukar aka amince da sabon kundin tsarin mulkin, suna fatan samun karin wasu kujeru a zaben Majalisun dokokin kasar da za'a gudanar nan da watanni biyu, inda suka yi amannar cewa yunkurin da shugaba Morsi yayi a baya baya nan na ba kansa karin iko ya sa sun samu karin magoya baya.