Mario Monti ya bayyana matsayinsa

Mario Monti
Image caption Praministan Italiya

Praministan kasar Italia na rikon kwarya, Mario Monti, ya ce ba zai tsaya takara a zaban da aka ce za ayi ba a watan Fabreru, amma ya ce a shirye yake a ko da yaushe domin jan ragabar gwamnati a nan gaba.

Mr Monti ya fadi a wajan taron manema labarai cewa baya san hada kansa da jam'iyyun siyasa.

Mr Monti ya ce a shirye ya ke ya bada shawara da karfin guiwa, idan kuma ta kama har da shugabanci.

Ya kuma kara da cewa yin watsi da shirinsa na tsuke bakin aljihu zai zama babbar illa ga kasar Italiya.

A ranar Juma'a ne Mr Monti ya yi murabus bayan da mutumin da ya gada, Silvio Berlusconi ya janye goyan bayansa ga gwamnatin da ke cike da kwararru.