An ci gaba da rusa hubbarai a Tumbuktu

'Yan tawayen Mali
Image caption Rusa hubbarai a Tumbuktu

Rahotanni daga arewacin Mali sun ce masu kaifin kishin Islama dauke da makamai da ke da mulki a yankin sun lalata hubbarai da dama a birnin Tumbuktu.

Wani shugaban kungiyar masu kaifin kishin Islaman ya shaidawa kamfanin dillanci labarai na Faransa cewa za ayi raga-raga da baki dayan habbaran dake Tumbuktu saboda sun sabawa musulunci.

A farkon wannan shekarar ma an rusa hubbarai da dama a birnin, wanda waje ne na tarihi da da majalisar dinkin duniya ta kebe.

Masu kaifin kinshin Islama da 'yan tawaye sun kwace iko da arewacin Mali bayan juyin mulkin da akai a farkon wannan shekarar.

A ranar alhamis ne majalisar dinkin duniya ta amince da kudurin tura dakarun soji karkashin jagorancin kasashen Afurka zuwa yankin.

Karin bayani