Ana jiran sakamakon zabe a Masar

Zaben raba gardama a kasar Masar
Image caption Zaben raba gardama a kasar Masar

An jinkirta bayyana sakamako a hukumance na zaben raba-gardamar da aka gudanar a Masar kan kundin tsarin mulki.

Wani jami'in hukumar koli ta zabe ya ce har yanzu hukumar na ci gaba da bincike kan karar da aka shigar da kuma zargin aikata ba daidai ba a lokacin zaben.

Ya ce a yanzu za a bayyana sakamakon ne a gobe Talata.

Sai dai a fili take cewa wadanda ke goyon bayan kundin tsarin mulkin ne zasu yi galaba da babban rinjaye.

Idan aka amince da kundin tsarin mulkin, hakan zai ba al'umar Masar damar zaben sabuwar majalisar dokoki da kuma kafa sauran hukumomin tafiyar da mulki.

Jagoran 'yan adawa na jam'iyyar Tsarin mulki ta Masar, Muhammad El Baradei, ya ce, kan al'ummar kasar yayi matukar rabuwa, kuma idan aka amince da kundin, kuma bisa dukkan alamu za a yi, lamarin zai janyo hatsaniya.

'Yan adawa na cewa kundin tsarin mulkin yana kunshe ne da ra'ayoyin 'yan kishin Islama, sun kuma bukaci hukumar zabe da ta gudanar da bincike kan zargin tafka kurakurai a lokacin zaben.