An kashe 'yan fashin kan teku

'Yan fashin Teku na Somalia
Image caption 'Yan fashin Teku na Somalia

Mahukunta a yankin Puntland mai cin kwarya-kwaryan gashin kansa a Somalia sun ce sun samu an sako sama da mutane ashirin da 'yan fashin kan teku ke tsare da su kusan shekaru ukun da suka wuce.

Har ila yau sun ce dakarun tsaron jiragen ruwa sun sako jirgin ruwan dakon mai dake dauke da tutar Panama, wato MV Iceberg One, kuma ba ayi amfani da karfi ba wajan sako jirgin.

Sun ce mutanan da aka tsaran sun nuna alamun inda aka azabtar dasu.

Wakiliyar BBC ta ce da yawansu basu da lafiya, wanda ba abun mamaki ba ne ganin cewa tun watan Maris na shekara ta 2010 ake tsare da su.

Kusan makwanni biyun da suka wuce ne aka fara yunkurin ceto mutanan lokacin da jami'an tsaron suka kashe 'yan fashin cikin tekun da dama wadanda ke kai makamai cikin jirgin ruwan da suka kwace.