Siriyawa da dama sun hallaka a layin biredi

Gidan gasa biredi a Syria
Image caption Mutane sun mutu a gidan biredi a Syria

Hotunan bidiyo da aka sanya a shafin Intanet sun yi nuni da gawawwakin mutane cikin mummunan yanayi watse akan tituna.

Masu aikin ceto dai sun yi ta saba wadanda suka sami munanan raunuka a bayansu, da kuma akan babura da manyan motocin daukar kaya , dama duk wani abu da za a iya amfani da shi wajen daukar su daga mummunan yanayin da suka samu kansu ciki, a lokacin da jiragen gwamnatin Syrian suka kai hari kan cincirindon layin mutane a wani gidan gasa biredi dake wajen garin, kamar yadda kungiyoyin kare hakkin dan adama suka bayyana.

Halfaya dai na daya daga cikin garuruwa a yankin da 'yan tawaye suka kwace a makon daya gabata, a fafutukar da suke na karbe ikon gabakidayan lardin.

Kuma kamar yadda yasha faruwa a lokuta da dama a baya, gwamnatin Syria ta maida martanin kwace wannan gari ta hanyar kaddamar da wani gagarumin hari inda ta bude wuta akan yankunan da suka kubuce daga hannunta.

Wannan al'amari dai na zuwa ne a yayinda manzon kasashen duniya na musamman Lakdar Brahimi ke ziyara a amascus.

Karin bayani