Lakdar Brahimi ya gana da shugaba Assad na Syria

Lakdar Brahimi
Image caption Lakdar Brahimi

Wakilin musamman na kasashen duniya a Syria, Lakhdar Brahimi ya gana da shugaba Bashar al-Assad a kwana na biyu na ziyarar da yake a Damascus.

Mr Brahimi ya ce har yanzu halin da ake ciki na damuwa ne.

Ya ce sun tattauna kan wasu hanyoyin da za a iya dauka domin kyautatuwar al'amurra, amma bai bada karin haske ba.

Shugaba Assad ya ce yana goyon bayan dukkan wani mataki da zai kare 'yancin kasar Syria.

Masu aiko da rahotani sun ce babu wasu alamu dake nuna cewa ana samun ci gaba a kokarin lalubo hanyoyin warware rikicin kasar ta Syria.