Yau ce ranar bikin kirsimeti

Paparoma Benedict

Yau ashirin da biyar ga watan Disamba, rana ce da mabiya addinin Kirista a sassa daban-daban na duniya ke gudanar da bikin kirsimeti, domin murnar tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu.

A lokacin wannan biki kuma mabiya addinin Kirista kan gudanar da hidimomi na ibada cikin farin ciki.

To sai dai wani babban kalubale da kan taso a duk lokacin da wannan muhimmin biki ya karato shi ne, karin afkuwar miyagun laifuffuka musamman a yankin kudu maso gabashin Najeriya wanda hakan kan zama wata barazana ga mutanen yankin wadanda kan so komawa gida daga wasu wurare don gudanar da shagalin wannan biki.

Ko da yake dai a lokuta da dama jami'an tsaro kan bayar da tabbacin irin kokarin da suke na samar da matakan tsaro.