Swaziland ta haramta fatari

Matan Swaziland yayin wani bikin gargajiya
Image caption Dokar ba ta shafi shigar da mata kan yi lokacin bukukuwan gargajiya ba

Rundunar 'yan sanda a kasar Swaziland ta ce za ta fara aiki da wata doka wadda ta haramta wa mata sanya fatarin da ya dangale a kasar.

Rundunar 'yan sandan kasar ta Swaziland ta yi gargadin cewa matan kasar da ke sanya dan tofi ko dangalallen fatari su fahinci cewa tsautsayin kame na zazzaga kansu.

Kazalika dukkan matan da ke sanya kananan riguna masu nuna tsiraici da ba sa rufe cibiya su ma za su fuskanci fushin hukuma.

Kakakin rundunar 'yan sandan kasar, Wendy Hleta, ta bayyana cewa 'yan sanda za su yi amfani da wata dokar kasar da aka kafa tun a shekarar 1889, wadda ta haramta shiga irin ta rashin mutunci a duk lokacin da aka koka musu da cewar wata ta yi wannan shigar.

Ta ce irin shigar da matan kan yi tamkar share wa masu fyade ne hanyar yin aika-aikarsu cikin sauki.

Wendy Hleta ta kara da cewa irin wannan shiga ta kaya shara-shara da tofin da ba ya rufe kafa kan sa wasu mazan yi wa matan kallon kare tanadi.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ta kara da cewa an dauki lokaci ba a hukunci da dokar, sai dai yanzu rundunar na so ta ankarar da mata game da wanzuwar dokar.

A cewar rundunar duk wadda aka cafke ta yi mummunar shiga irin ta ballagaza, wato da dangalallen tofi ko riga mai nuna tsiraici to za a yi mata tarar dala goma ko fam shida ko kuma daurin wata shida idan ta kasa biyan tarar.

'Yan sandan kasar dai sun jaddada cewa ba nufinsu ne su kuntata wa mata ba, face su kyautata tarbiyyar al'umar kasar.

Sai dai kuma wani abu mai kama da an yi ba a yi ba shi ne kakakin ta yi bayanin cewa dokar ba za ta shafi irin shigar da mata kan yi a lokutan bukukuwa irin na gargajiya ba ko da kuwa tofin da mata suka sa dangalalle ne. Haka kuma dokar ba ta shafi suturar da mata masu shayarwa ke sanyawa ba ko da kuwa suna nuna tsiraici saboda lalurar shayarwa.

Kasar Swaziland dai ita kasa daya tilo a Afirka kudu da Sahara da basaraken gargajiya ke mulkinta. Sarkin yana da mata goma sha uku, kuma ana zarginsa da son rayuwa irin ta garari ko fantamawa.