An kashe wasu ma'aikatan kashe gobara biyu Amurka

Bindiga a kan tutar Amurka
Image caption Bindiga a kan tutar Amurka

An kashe wasu ma'aikatan kashe gobara biyu, aka kuma raunata wani, lokacin da aka bude masu wuta, bayan sun kai dauki sakamakon wata gobara da ta tashi a jihar New York ta Amurka.

Jami'an 'yan sanda sun ce dan bindigan mai suna William Spengler mai shekaru sittin da biyu ya kashe maaikatan ne bayan da yayi musu kwantan bauna a lokacin da suka zo don kashe gobarar, inda kuma ake kyautata zaton cewa daga bisani kuma ya kashe kansa.

An dai daure Mr Spengler ne a shekarar alif dari tara da tamanin da daya a gidan yari bayan da aka same shi da laifin kashe kakarsa inda aka yanke masa hukuncin daurin shekaru goma sha bakwai.

A wani taron manema labaru, shugaban rundunar 'yan sanda Gerald Pickering ya bayyana cewa dan bindigan mutum ne dake da matsaloli sosai, inda kuma ake kyautata zaton cewa ma yana da tabin hankali.

Kawo yanzu dai ba'a san in da 'yar uwar dan bindigan ta shiga ba, inda jami'an 'yan sanda ke fargabar cewa mai yiwuwa ta kone cikin gidaje bakwai din da suka kama ne da wuta.

Wannan al'amari dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tafka muhawara akan batun takaita mallakar bindigogi a Amurka bayan kisan gillar da wani dan bingida yayi a makarantar Newtown inda mutane ashirin da takwas suka mutu a farkon wannan watan.

Karin bayani