An amince da sabon kundin tsarin mulkin Masar

Sakamakon zaben Masar
Image caption Sama da kashi sittin cikin dari sun amince da tsarin mulki

Hukumar shirya zabe a Kasar Masar tace kusan kashi sittin da hudu cikin dari na masu kada kuri'a ne su ka amince da sabon daftarin mulkin kasar mai cike da kace nace.

An dai gudanar da zaben jin ra'ayoyin jama'a ne kashi biyu--- a ranakun sha biyar da ashirin da biyu ga watan Dismaba

Yayin da yake sanar sa sakamakon zaben, Alkali Samir Abu el-Maati yace hukumar ta gudanar da bincike akan dukkanin korafe korafen magudin zabe.

Daftarin tsarin mulkin dai yana da goyan bayan Shugaba Morsi da 'yan uwa musulmi na Muslim Brotherhood.

Kuma zai bada damar zabar sabbin 'yan majalisar dokoki.

Sai dai 'yan adawa sun soki yadda aka gudanar da zaben

Karin bayani