Shugaba Morsi ya yi jawabi ga al'ummar Masar

Shugaba Muhammad Morsi na Masar
Image caption Shugaba Muhammad Morsi na Masar

Shugaba Morsi na Masar ya yi wa al'ummar Kasar jawabi a gidan talabijin na kasar, bayan da masu jefa kuri'a suka amince da sabon kundin tsarin mulkin Kasar mai cike da kace nace a karshen mako

Mr Morsi ya ce zai kirkiro da wasu manyan ayyuka da nufin ciyar da tattalin arzikin kasar gaba.

Shugaban na Masar ya kuma ce ya fahimci cewar wasu sun kada kuri'arsu ta rashin amincewa da tsarin mulkin, amma ya ce hakan wata alama ce dake nuna al'umma ta dimokradiya

Ya kuma yi kira ga dukkanin bangarorin siyasar Kasar da su shiga tattaunawa, da kuma cigaba da abinda ya kira wata sabuwar taswira ta tafiya ga Kasar ta Masar.

Amincewa da kundin tsarin mulki shi zai share fagen zaben majalisar dokoki. a Masar cikin watani biyu masu zuwa.

'Yan adawa sun ce zasu ci gaba da gwagwarmayar nuna adawa a yakin neman zabe, da kuma a majalisar dokoki.

Karin bayani