Gobara ta tashi a unguwar Jankara dake Lagos

Najeriya
Image caption Gobara ta lalata gine gine a Lagos

Wata mahaukaciyar gobara ta tashi a wani dakin dake ajjiye kayayyakin wasannin tartsatsin wuta a Lagos, birni mafi girma a Najeriya.

Mutane da dama sun samu raunuka yayinda wasu rahotannin da ba tabbatar ma ke cewa akalla mutane 15 ne su ka gamu da ajalin su.

Shaidu sunce wutar ta haifar da rudani, kuma magidantan yankin sun taimakawa masu kashe gobara yayinda kayayayyakin wasannin tartsatsun wutar ke cigba da fashewa a ginin dake cin wutar.

Ma'aikatan kai agajin gaggawa sunce sun samu matsala wajen kaiwa ga inda wutar take ci, sabooda cincirindon mutanen da sukai dafifi a ginin.

Wasannin wuta dai wani al'amari ne da ake yawan gani a Najeriya a lokutan bukukuwan Kirsimeti da kuma na sabuwar shekara

Karin bayani