Mummunan yanayi ya durkusar da harkoki a Amurka

Image caption Barack Obama

Mummunan yanayi na tsananin zubar dusar kankara da mukumukun sanyi sun gurgunta al'amura a sassan Amurka lamarin da ya haifar da guguwa da tsawa sau kusan talatin.

Mutane sama da dubu 200 ba su da wutar lantarki, akasarin su a jihar Arkansas.

Lamarin ya yi sanadiyar soke tashin jiragen sama 1500 a ranar Laraba kadai.

Ababan hawa da bishiyoyi sun yi ta faduwa , abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Masu hasashen yanayi sun ce za a fuskanci irin wannan yanayi a sassan arewa maso gabashin Amurka inda aka yi hasashen zubar dusar kankara mai yawan gaske da takai tsawon santimita 40.