Ana zaman dar-dar a birnin Bangui

'Yan tawayen Afrika ta Tsakiya
Image caption 'Yan tawayen na zargin gwamnati da rashin mutunta yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a shekarar 2007

An shiga zaman dar-dar a Bangui, babban birnin Afrika ta Tsakiya, yayin da 'yan tawaye ke dumfarar birnin.

Wata jami'ar Majalisar Dinkin Duniya, Margaret Vogt ce ta bayyana hakan.

Jami'ar ta shaida wa BBC cewa ta ga mazauna birnin na Bangui sun shiga dimuwa game da abin da zai faru.

A halin yanzu dai majalisar ta fara kwashe ma'aikatanta da ayyukansu ba su zama wajibi ba daga Afrika ta Tsakiya.

Yayin da Kasar Amurka ita ma ta bukaci 'yan kasarta su bar Afrika ta Tsakiyar.

Faransa na da dakaru 200

Kasar Faransa kuwa ta tsaurara matakan tsaro a ofishin jakadancinta dake Bangui, bayan masu bore sun kai masa hari.

Masu zanga-zangar sun yi ta jifan ofishin da duwatsu, kuma suka yaga tutar Faransa.

Suna neman Faransa ta kai musu dauki wajen murkushe 'yan tawayen arewacin kasar, kana suna zargin Faransar da yin biris da kasar da ta goya.

Faransar dai nada dakaru 200 a Afrika ta Tsakiya, kuma gwamnatin Bangui ta bukaci Faransa ta taimaka waje murkushe 'yan tawayen da tuni suka riga suka kwace wasu garuruwan dake arewacin kasar.

Sai dai shugaban Faransa Fancios Hollande ya yi watsi da batun kai musu dauki.

Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Faransa ya gayawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, rikicin Afrika ta Tsakiya na bukatar a warware shi ta hanyar tattaunawa.