Za a binciki manyan 'yan adawar Masar

Shugaba Morsi na Masar
Image caption An zargi 'yan adawa da yunkurin kifar da gwamnatin Morsi

Babban mai shigar da kara na Masar ya bada umarnin gudanar da bincike kan wasu shugabannin 'yan adawar kasar game da yunkurin ganin an hanbarar da gwamnatin shugaba Muhammad Morsi.

Talat Ibrahim Abdallah wanda shugaban Kasar ya nada wannan mukami a watan da ya gabata, ya sanya hannu kan wannan umarni akan wasu shugabannin 'yan adawa uku.

Ciki harda Mohammed El Baradei, da tsohon sakatare janar na kungiyar Kasashen Larabawa Amr Moussa da kuma tsohon dan takarar shugabancin Kasar Hamdeen Sabahi.

Shugabannin 'yan adawar uku dai, sun kafa wata gamayyar 'yan adawa da ake kira National Salvation Front, domin yiwa shugaban Kasar bore, bayanda ya baiwa kansa wasu jerin iko.

Masu aiko da rahotanni dai na cewa akwai yiwuwar binciken, zai kara janyo rarrabuwar kai ne a cikin Kasar.

Sai dai wannan sanarwa bata nufin cewa za a tuhumi mutanen uku a gaban kotu.

Karin bayani