Masu noman gahawa sun kona shugabansu a India

Wata mata na aiki a gona ganyen shayi a India
Image caption Rabin ganyen shayin da Inda ke fitar wa ana noma shi ne a Assam

Daruruwan masu noman ganyen shayi a jihar Assam dake kasar India, sun kona mutumin da ya dauke su aiki, Mridul Kumar Bhattacharyya ta hanyar cinna wa gidansa wuta.

Jami'ai a jihar dake arewa-maso gabashin kasar sun ce lamarin ya rutsa da matarsa wacce ita ma ta rasa ranta.

Bayan shafe mako biyu suna jayayya da hukumar dake gudanar da makekiyar gonar ne, ma'aikatan suka yi wa gidan mai gonar zobe sannan suka sa wuta a ranar Laraba.

'Yan sanda sun ce lamarin ya auku ne bayan hukumar ta bukaci wasu ma'aikata su bar gidajen da suke ciki.

Wata jami'ar a karamar hukumar, Meenakshi Sundaram ta ce manoman da suka yiwa gidan mai gonar tsinke sun kai kusan 700.

Haka kuma tace sun kona motocin mutumin guda biyu, kuma an gano gawawwakin mutumin da na matarsa Rita a baraguzan gidan.

'Yan sanda sun kama ma'aikata uku da ake zargi da hannu a al'amarin.

Hari kan masu gonaki

Mista Bhattacharyya ya taba fuskantar zanga-zanga daga manoman dake masa aiki a wata gonar ganyen shayinsa ta daban, shekaru biyu da suka wuce.

A wancan lokaci manoman a fusace sun cinna wa gonar wuta, bayan zargin cewa ya yi harbi a lokacin da suke bore a kofar gidansa bisa rahoton kaiwa wata mata hari.

Fiye da rabin ganyen shayin da India ke fitar wa kasashen waje, ana noma shi ne a manyan gonaki 800 dake Assam.

Ana samun rahotannin kai farmaki kan masu manyan gonakin shayi a jihar Assam dake kasar ta India a 'yan shekarun baya-bayan nan.