Shugaban Iran ya kori ministar lafiya

Ministar lafiya a Iran
Image caption Ana fama da karancin magunguna a Iran

Shugaban Iran Mahmud Ahmadinaj ya kori Ministar lafiyar Kasar, kuma ita ce mace kadai a majalisar zartarwar kasar.

Ba a dai bada dalilin korar ministar Marzeih Vahid ba a hukumance .

Sai dai tunda farkon makon nan, Ministar tayi gargadin karancin magunguna a asibitoci sakamakon takunkumin da kasashen duniya suka sanya wa Kasar, amma Mr. Ahmadinaj ya musanta hakan, yana mai cewa babu wanda keda 'yancin yin magana a akan wani karanci

Iran dai na samar da magungunan ta, amma tana shigo da sinadaran hada magungunan ne daga waje