'Sojoji sun kai sumame a Kaduna'

Jihar Kaduna
Image caption Kaduna na daga cikin jihohin da ke fama da hare-hare a Najeriya

Mazauna unguwar Rigasa a jihar Kaduna sun shaida wa BBC cewa "an shafe sa'o'i ana harbe-harbe bayan da sojoji suka kai sumame wani gida a unguwar".

Rahotanni sun ce tun da misalin karfe hudu na asubahi ne ake ta bata-kashi tsakanin jam'ian tsaro da wasu mutane da ke zaune a cikin wani gida.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce an samu asarar rayuka a lamarin, sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan.

Kawo yanzu dai jami'an tsaro basu ce komai ba game da wannan lamari.

Wakilin BBC a Kaduna Nura Muhammad Ringim, ya ce unguwar ta Rigasa ta yi kaurin suna wurin tashe-tashen hankula a baya.

Kuma an sha kai hare-hare kan jami'an tsaro da masu unguwanni a yankin, a cewar wakilin na mu.

Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren da a wasu lokutan ake alakanta wa da kungiyar nan ta Boko Haram.

Karin bayani