Majalisar Dinkin Duniya za ta janye ma'aikata

Image caption Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon

Majalisar Dinkin Duniya da Amurka sun ce za su kwashe ma'aikatansu wadanda ayyukansu ba su zama na wajibi ba daga jamhuriyar Afirka ta tsakiya, inda gamayyar kungiyoyin 'yan tawaye ke yunkurin kwace babban birnin kasar, Bangui.

'Yan tawayen kasar sun ce ba su da niyyar shiga babban birnin sai dai wadansu sakonni da ke cin karo da juna sun tilastawa Majalisar Dinkin Duniya da Amurka daukar matakan kare ma'aikatansu.

Sakonnin dai na cewa a shirye gwamnatin kasar take ta sasanta da 'yan tawayen ba tare da gindaya sharuda ba, yayin da ita kuma gamayyar 'yan tawayen da ke dauke da makamai ke ci gaba da tunkarar babban birnin duk kuwa da nanatawar da ta yi cewa ta dakatar da kai hare-hare.

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya a kasar, Margaret Vogt, ta ce ba su gamsu da wadannan kalamai ba, kuma hakan ne ya sanya Majalisar ta sanar cewa daruruwan ma'aikatanta za su fice daga kasar, ko da halin da ake ciki ka iya munana.

Tuni dai kasar Faransa ta aike da dakarunta zuwa kasar domin kare ofishin jakadancinta da ke babban birnin, bayan 'yan kasar sun gudanar da wata kazamar zanga-zanga, suna masu zarginta da gaza dakatar da 'yan tawayen da ke yunkurin kwace birnin.