An kashe akalla mutane 17 a Najeriya

Nigeria
Image caption Najeriya na fama da matsalolin tsaro a sassan kasar da dama

Rahotanni a Najeriya na cewa mutane akalla 17 sun rasa rayukansu wasu da dama kuma suka jikkata ciki harda jami'an tsaro a hare-hare daban-daban a wasu jihohi na arewacin kasar.

Lamuran dai sun faru ne a jihohin Borno, inda aka rawaito wasu samari 'yan bindiga sun hallaka Alhaji Abubakar Girgir wani hamshakin dan kasuwa, da wasu masu gadi farar hula su uku.

Rahotanni sun ambato kakakin rudunar 'yan sandan jihar ta Borno, Gedion Jibrin, na cewa wasu 'yan bindigar sun kashe wasu farar hula su bakwai a karamar hukumar Jere, amma dai bai yi wani karin haske kan lamarin ba.

A Jihar Adamawa, wasu mahara masu yawan gaske da bindigogi a motoci da babura sun kona gine-gine da dama na hukuma da suka hada da na 'yan sanda da bangaren shari'a.

Hakazalika a jihar Filato, mutane akalla hudu ne suka rasa rayukansu a yankin Bachit da ke karamar hukumar Riyom.

Lamarin ya faru ne sakamakon fada tsakanin 'yan kabilar Berom da Fulani inda kakakin rundunar tsaro ta musamman mai aikin kiyaye zaman lafiya a jihar, ya shaida wa BBC cewa sun kame mutane biyu.

Karin bayani