Bikin tunawa da Benazir Bhutto ta Pakistan

Bilawal Zardari
Image caption Bilawal shi ne shugaban jam'iyyar PPP tun bayan da aka kashe mahaifiyarsa a 2007

Dan tsohuwar Fira Ministar Pakistan Benazir Bhutto ya sha alwashin yakar kungiyoyin masu fafutuka domin tabbatar da tsarin demokuradiyya a kasar.

Bilawal Bhutto Zardari ya fada wa magoya bayan jam'iyyarsa da ke gangamin tuna shekara biyar da mutuwar mahaifiyarsa cewa "ta sadaukar da rayuwarta domin tabbatar da tsarin demokuradiyya".

An kashe Ms Bhutto ne a wani harin bam da kuma bindiga a lokacin da take yakin neman zabe a shekara ta 2007.

Danta wanda mahaifinsa shi ne shugaba Asif Ali Zardari, baya bayyana kansa sosai a matsayinsa na shugaban jam'iyyar.

'Hasken demokuradiyya'

A jawabin da ya yi wanda aka watsa a gidan talabijin na Pakistan, Mr Bhutto Zardari ya shaida wa dubun dubatar magoya bayan jam'iyyar Pakistan People's Party (PPP) a kusa da hubbaren danginsu a lardin Sindh cewa "mutane sune gwamnati".

"Hasken demokuradiyya za ta ci gaba da haskakawa," kamar yadda ya ce, yana mai alwashin cewa jam'iyyarsa za ta yaki kungiyoyin masu fafutuka da tsattsauran ra'ayi domin tabbatar da zaman lafiya da kuma tsarin demokuradiyya.

Bilawal mai shekaru 24, wanda ya yi karatun digiri a jami'ar Oxford ta Ingila, shi ne shugaban jam'iyyar PPP tun bayan da aka yiwa mahaifiyarsa kisan gilla a shekara ta 2007.

A yanzu dai ba zai iya tsayawa takarar kowanne mukami ba sai ya cika shekaru 25 da haihuwa.

Karin bayani