Matashiyar da aka yi wa fyade a India ta rasu

Image caption Manmohan Singh

Matashiyar nan 'yar kasar India, wacce aka yi wa fyade kuma aka ji mata munanan raunuka a wata motar bus a birnin Delhi, ta rasu ranar Asabar a kasar Singapore inda aka kai ta domin yin jiyya.

Hukumomin asibitin da aka kwantar da ita sun ce matashiyar, wacce ba a bayyana sunanta ba, ta rasu ne bayan wadansu sassan jikinta da kwakwalwarta sun daina aiki.

Sun ce raunukan da ta samu lokacin da ka yi mata fyade ne suka ta'azzara yanayin da ta shiga.

Labarin mutuwar ta ya janyo kakkausar suka daga 'yan kasar.

Tsoron barkewar tarzoma

An ce an yi wa matashiyar, mai shekaru 33 a duniya, wacce ke karanta aikin likita fyade sau da dama, kana aka yi ta dukanta da wani karfe, yayin da kuma aka jefar da ita daga cikin bus.

Tuni dai aka kama wandansu mutane shida wadanda ake zargi da aikata wannan aika-aika.

Cin zarafin da aka yi wa matashiyar ya janyo munanan zanga-zanga a India, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wani dan sanda.

Firayim Ministan kasar, Manmohan Singh, ya bayyana bakin cikinsa da jin wannan labarin mutuwar, kana ya ce abin da ya rage yanzu shi ne 'yan kasar su dauki matakin hana sake aukuwar wannan lamari.

'Yan sanda a birnin Delhi sun sanya shingaye a ofisoshin gwamnati da ke tsakiyar birnin domin gudun barkewar tarzoma.

Karin bayani