An sanya hannu a dokar tsarin iyali a Philippines

Image caption Benigno Aquino

Shugaban Philippines, Benigno Aquino, ya sanya hannu a kan wata dokar tsarin iyali wacce aka kwashe shekaru 14 kafin a sanya ma ta hannu.

Dokar za ta bai wa iyalai damar samun kulawa a duk fannin kayyade iyali amma ban da magungunan zubar da ciki.

Philippines ce kasar da aka fi yawan haihuwa a kudu maso gabashin Asia.

Masu goyon bayan wannan doka na fatan cewa wannan mataki zai rage yawan haihuwa da talauci a kasar.

Dokar ta fuskanci kakkausar suka daga 'yan majalisa da ke jami'iyun adawa, da kuma cocin Roman Katolika.

Limaman coci-coci sun sha alwashin kalubalantar wannan mataki a kotun koli ta kasar.

Karin bayani