Mayakan Darfur sun kwace sansanonin soji

Mayakan Darfur
Image caption Mayakan Darfur

'Yan tawaye a yankin Darfur na kasar Sudan sun kwace wasu muhimman sansanonin soji guda biyu daga hannun dakarun gwamnati.

Gungun 'yan tawayen na bangaren kungiyar Sudan Liberation Army da Abdul Wahid al Nur ke jagoranta sun ce sun kwace sansanonin garin Nertiti da yankin Jebel Marra.

Kakakin 'yan tawayen ya ce sun kashe dakarun gwamnati da dama a hare-haren.

Sai dai babu wata kafa mai zaman kan ta da ta tabbatar da wannan rahoton.

Wasu daga cikin kungiyoyin mayakan da ke Darfur sun yi sulhu da gwamnatin Sudan a bara yayinda wasu kuma suke cigaba da fafatawa.