Shugaba Bozize ya amince da 'yan tawaye

Shugaba Francois Bozize
Image caption Shugaba Francois Bozize

Shugaban kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Francois Bozize ya ce a shirye ya ke ya kafa gwamnatin hadin kasa tare da gungun 'yan tawayen da suka kwace garuruwa da dama, ciki har da garin da ke da nisan kilomita dari da hamsin daga Bangui, babban birnin kasar.

Mr. Bozize, wanda ya yi jawabi bayan ganawa da shugaban kungiyar gamayyar kasashen Afrika, Boni Yayi yace ba zai sake tsayawa takara a shekarar dubu biyu da sha shida ba.

'Yan tawayen sun shaidawa BBC cewa zasu tattauna game da tayin shugaban kasar.

A ranar Asabar ne dai 'yan tawayen suka kwace garin Sibut, mai nisan kilomita dari da hamsin daga babban birnin.

An sake tura wasu sojojin kasar Gabon zuwa Bangui babban birnin Janhuriyar Afurka ta tsakiyar ranar Asabar, domin zama cikin shirin ko ta kwana.

Kasar Faransa dai ta tsaya kai da fata cewa zata shiga rikicin ne kawai domin ta kare lafiyar 'yan kasarta-- amma ba wai gwamnatin ba.

Wani babban jami'in MDD ya shaidawa BBC cewa an kwashe baki dayan ma'aikatansu zuwa kasar Kamaru dake makwabtaka da ita.