Yunkurin ceto tattalin arzukin Amurka

Majalisar Dokokin Amurka
Image caption Majalisar Dokokin Amurka na zama na musamman

Yan majalisar dokokin Amurka na daukar matakai a karo na karshe domin dakatar da dokar rage kashe kudin gwamnati da kuma karin haraji wadda za ta fara aiki ranar daya ga watan Janairu.

A wani yanayi na ba-saban ba, majalisun dokokin na zaman muhawara a yammacin Lahadin nan.

Manufar zaman dai ita ce kare Amurka daga fadawa cikin halin tsaka-mai-wuyar karayar tattalin arziki - sanadiyyar karin haraji da dakatar da kashe kudin da adadinsu ya kai dala biliyan dari shida.

Ganin yadda kwanaki biyu ne kawai ya rage wannan doka ta fara aiki da yawan Amurkawa na ganin zai yi wuya a samu dai daito a majalisar.

Ko dayake, a wata hira da akai da shi a gidan talabijin na NBC, shugaba Obama ya ce lallai akwai sauran lokaci da za'a iya yin gyara.

Karin bayani