Bikin sabuwar shekara a Burma

Bikin sabuwar shekara a Burma
Image caption Bikin sabuwar shekara a Burma

A karan farko kasar Burma zata tari sabuwar shekara da kidayar 'yan dakikokin da suka rage a shiga sabuwar shekarar a bainar jama'a tare dayin wasannin tartsatsin wuta.

Wannan dai wata alama ce ta nuna cewa rayuwar jama'a na sauki ta fuskar siyasa.

A karkashin mulkin soji dai an hana jama'a taro a irin wannan lokaci, to amma yanzu ana sa ran dubban 'yan kasar Burma za su taru a Rangoon, birni mafi girma a kasar domin kallon wasannin tartsatsin wutar da za'a yi.