Alkawarin Bozize ga 'yan tawaye

Yayi Boni da Francois Bozize
Image caption Yayi Boni da Francois Bozize

'Yan tawaye a jamhuriyar Afrika ta tsakiya wadanda suka doshi babban birnin kasar wato Bangui, sun ki amincewa da tayin da shugaban kasar, Francois Bozize ya yi musu.

Bayan tattanawarsa da shugaban kungiyar tarayyar Afrika wato AU, Mista Yayi Boni, shugaban na jamhuriyar Afrika ta tsakiya ya yi tayin kafa gwamnatin hada kan kasa tare da 'yan tawaye, sannan kuma ba zai tsaya zabe ba a shekara ta 2016.

Wani kakakin 'yan tawayen, Eric Massi, ya ce da wuya a yarda da shugaban kasar sabili da dakarun tsaronsa na ci gaba da kai hari kan magoya bayan 'yan tawayen da ke Bangui.

A cewarsa, mogoya bayan 'yan tawayen fiye da dari hudu ne suka yi batan dabo a birnin.

Gwamnatin dai ta musanta cewa tana da hannu a bacewarsu.

Mista Massi ya ce ya kamata a tura wata rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasashen Afirka don ta hana abin da ya kira ganawa 'yan kabilun arewacin kasar wadanda 'yan tawayen suka fito daga cikinsu ukuba.

Idan ba haka ba kuma, a cewarsa, 'yan tawayen za su shiga birnin na Bangui don ba su kariya.

Tuni dai hankula suka tashi a birnin na Bangui yayin da ake jira a ji martanin na 'yan tawaye.

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai, 'yan tawayen suka kwace garin Sibut mai nisan kilomita 150 daga babban birnin kasar wato Bangui.