Gwamnatin Pakistan ta saki 'yan Taliban hudu

taliban
Image caption 'Yan Taliban na tada zaune tsaye a Afghanistan

Wani jami'in gwamnatin Pakistan ya ce an saki wasu 'yan kungiyar Taliban ta Afghanistan su hudu daga gidan yari.

A cewarsa mutanan sun hada da tsohon ministan shari'a, Mullah Nooruddin Turabi, wanda ke fama da matsananciyar rashin lafiya.

A watan da ya gabata ma Pakistan ta saki 'yan kungiyar Taliban ta Afghanistan din akalla su tara a wani yunkuri na taimakawa a sansanta tsakanin kungiyar Taliban din da gwamnatin Afghanistan.

Sai dai har yanzu ana ci gaba da tsare wani jagoran Taliban din a Pakistan, wato Mullah Abdul Ghani Baradar, wanda shine mataimakin shugaban Taliban, duk da irin godon da gwamnatin Afghanistan din ke ta yi na a sake shi.