'Yan siyasar Amurka na neman mafita

Barack Obama
Image caption Shugaba Barack Obama na Amurka

'Yan siyasar Amurka za su kwashe yinin yau suna kokarin fahimtar juna a kan hanyar da za a bi don kaucewa wani jerin matakan tsuke bakin aljihun gwamnati da karin haraji wanda zai fara aiki a Sabuwar Shekara.

An dage wani zama na musamman na Majalisar Dattawa ba tare da cimma yarjejeniya ba.

Mutane da dama dai na fargabar cewa idan ba a samu daidaito ba, tattalin arzikin kasar ta Amurka zai sake fuskantar koma-baya.

Sai dai kuma bayan an shafe kwanaki ana zazzafar muhawara, rahotanni sun ce har yanzu akwai rashin fahimtar juna tsakanin 'yan jam'iyyar Democrat da takwarorinsu na jam'iyyar Republican a Majalisar Dattawan.

Shugaba Obama dai ya ce idan ba a cimma yarjejeniya ba zai gabatar da wani kudurin doka na wucin-gadi wanda zai tabbatar da cewa ba a karawa iyalai matalauta da masu matsakaicin samu kudin haraji ba.

Ana sa ran Majalisar Dattawan ta Amurka za ta sake zama nan gaba a yau.

Karin bayani