India ta kaddamar da shirin tallafa wa matalauta

Mabarata a India
Image caption Mabarata a India

Gwamnatin India ta kaddamar da wani sabon shirin biyan biliyoyin daloli don jin kai kai tsaye ga matalauta a wani kokari na kawar da cin hanci da rashawa.

A karkashin sabon shirin,za a rinka saka kudaden jin kan cikin asusun ajiyar bankunan mutanen da abun ya shafa domin hana jami'an da ke da cin hanci sace su.

Ministan kudi na India ya bayyana shirin a matsayin wani abun sauyin yanayi ga shugabanci.

To amma masu sukar shirin sun ce zai yi wuya a aiwatar da shi a kasar da mutane matalauta da yawa ba su da asusun ajiyar banki.