An kafa sabuwar kungiyar kyautata zaman tare a Kaduna

Muktar Ramalan Yero, Gwamnan Jihar Kaduna
Image caption Muktar Ramalan Yero, Gwamnan Jihar Kaduna

An kaddamar da wata sabuwar kungiya da keda aniyyar taimakawa wajen magance rigingimun addini da kabilanci a jahar Kaduna ta Najeriya.

Kungiyar mai suna "Christian Muslim alternative to conflict" a turance, - wato kungiyar samar da wata hanyar zama tare maimakon takaddama, na kunshe ne da manyan malaman addini kirista da na musulunci.

Suna dai ganin cewa sun gaji da rigingimun da a lokuta da yawa ke haifar da asarar rayuka da dukiyoyi da dama.

Shugabannin kungiyar sunce sun samu karfin guiwar kafa kungiyar ne bayan wani abun karamci da kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Jihar Kaduna ta yi lokacin da suka sayi shafi a wata jarida don nuna rashin jin dadinsu ga batancin da aka yiwa Annabi Muhammad (SAW).

Kungiyar ta bayyana cewar wasu ne ke haddasa rigingimun dake faruwa tsakanin Musulmi da Kirista domin amfanin kansa.

Ta kuma gargade su da su daina tun kafin asirinsu ya tonu. Sun yi zargin cewa yaudara da son kai ne suka hana dukanin kokarin baya na warware matsalar cimma nasara.