An kashe sojan Pakistan a Kashmir

Sojan Indiya na sintiri kan iyakar da ta raba Kashmir gida biyu
Image caption Sojan Indiya na sintiri kan iyakar da ta raba Kashmir gida biyu

Rundunar sojin kasar Pakistan ta ce dakarun sojin India sun kashe sojanta guda a yankin Kashmir da ake takaddama a kai.

Rundunar ta ce sojan nata, ya rasu ne bayan da dakarun India suka bude masa wuta ba gaira ba dalili a iyakar kasashen biyu.

Mutuwar sojan dai shi ne alamari na baya bayan nan wanda ya haddasa fito na fito.

Tun farko sojin India sun musanta rahotannin cewar sune suka haddasa arangamar ta hanyar kafa sababbin wuraren sa ido a kusa da kan iyaka -- wani lamarin da aka haramta a karkashin wani tsarin tsagaita wuta.

nsa.

Karin bayani