An kashe ma'aikatan bayar da agaji a Pakistan

Direban da ya tsallake harin da aka kashe ma'aikatan agaji a Pakistan
Image caption Direban da ya tsallake harin da aka kashe ma'aikatan agaji a Pakistan

'Yansanda a Pakistan sunce malaman makaranta 5 da kuma ma'aikatan lafiya 2 ne wasu yan bindigar da ba a san ko suwa nene ba a kan babur suka harbe har lahira.

Wani Jami'in yan sanda a garin Swabi na arewa maso yammacin kasar, Abdul Rasheed ya ce an kai wa ma'aikatan hari ne yayinda suke tafiya a mota daga wurin da suke aiki.

Daga cikin daliban akwai yan mata 150.

Dukanin cibiyoyin dake ilmantar da yan matan da kuma kungiyoyin dake gudanar da alluran riga kafin , a baya bayan nan sun zama abun hara ga yan gwagwarmayar musulunci na Pakistan.

A bangare daya kuma,Ma'aikatan kyon lafiya na Majalisar dinkin duniya a Pakistan sunce yara da yawan da ba a taba gani ba sun mutu sakamakon kyanda a shekara ta 2012.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce yara fiye da 300 ne suka mutu galibi a lardin Sindh na kudancin kasar a inda aka samu ambaliyar ruwa a cikin shekaru 3 jere.

Jami'ai suka ce,rashin abinci mai gina jiki ga yaran da abun ya shafa ya taimaka ga yawan mutuwar.

Hukumomin kiyon lafiya na Pakistan sun soma alluran riga kafin kamuwa da ciwon na Kynada a yankunan da lamarin ya fi shafa.

Karin bayani