An kashe wata yarinyar gida yar Sri lanka a Saudiya

Mahaifan Razina Nafeek da aka kashe a Saudiya
Image caption Mahaifan Razina Nafeek da aka kashe a Saudiya

Gwamnatin Sri Lanka tace ta yi tir da sare kan wata 'yar aikin gida yar Kasar ta Sri lanka da hukumomin Saudiya suka yi.

A cikin watan sanarwa, gwamnatin ta ce ta roki da a yafe wa Rizana Nafeek, wadda aka samu da laifin kashe wani yaro da take kula da shi a shekara ta dubu 2 da 5, wani laifin da ta musanta.

Wakilin BBC a Sri Lanka ya ce akwai shedar da ke nuna cewar Rizana Nafeek tana da shekaru 17 ne kawai a lokacin da aka yi zargin kisan -- wanda idan har gaskiya ne,Saudiya ta saba yarjejeniyar duniya kan hakkin yara wadda ta hana hukuncin kisa kan kananan yara da suka yi laifi.

Majalisar dokokin Sri Lanka ta yi tsit na minti biyu don jimamin Rizana Nafeek.

Karin bayani