"Bata-kashi tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram"

Matsalar tsaro a Najeriya
Image caption Ana zargin jami'an da wuce-gona-da-iri a wasu lokutan da dama

Rundunar tsaro ta hadin-gwiwa a jihar Borno ta Najeriya ta ce an kashe mata soja daya tare da raunata wasu biyu, yayin da ta kashe wasu 'yan kungiyar Boko Haram 13 a lokacin wata arangama da suka yi.

"Tun da misalin karfe hudu na yammacin ranar Talata ne rundunarmu ta yi arangama da wasu 'yan kungiyar Boko Haram a unguwannin Bulabulin da Bayan da ke Maiduguri", a cewar sanarwar da Kakakin rundunar tsaro Laftanar kanar Sagir Musa ya sanyawa hannu.

Sai dai kamar yadda sanarwar ta bayyana an samar da cikakkiyar kariya ga farar-hula al'umar gari saboda a cewar kakakin ba a taba ko da mutum guda ba.

Kawo yanzu dai babu wata sanarwar da ta fito daga kungiyar wacce aka fi sani da Boko Haram da ke ikirarin cewa da 'ya'yanta aka kara.

Harwayau rundunar ta ce ta yi nasarar kwato wasu makamai daga hannun 'yan bindigar da suka hada da bindigogi samfurin AK 47 guda uku, da roka daya, da kuma albarusai mahadin boma-bomai.

Sai dai kakakin ya ce akwai wasu daga cikin 'yan bindigar da suka arce, wadanda ya ce rundunarsu na ci gaba da farautarsu da zummar kwato makaman da ke hannunsu.

Karin bayani