An yi shelar zaman makoki a Ivory Coast

Turmutsutsu a Abidjan, babban birnin kasar Ivory Coast
Image caption Turmutsutsu a Abidjan, babban birnin kasar Ivory Coast

An yi shelar zaman makokin kwana uku a Ivory Coast, bayan mutuwar mutane da dama, a wani turmutsutsu, yayin bikin wasan wuta ranar jajibirin sabuwar shekara.

Akalla dai mutane sittin ne aka bayyana sun hallaka, yayinda da dama suka jikkata a lokacin turmutsutsun da ya faru, yayinda ake gudanar da bikin wasan wuta wanda gwamnatin ta shirya ranar jajjibirin sabuwar shekara.

Jami'ai sun ce akasari wadanda abin ya shafa matasa ne.

Akwai rahotanni masu saba wa juna dangane da abinda ya faru a yamutsin a kusa da dandalin wasanni dake Abidjan babban birnin kasar.

Wasu da suka shaida lamarin sun ce mutane sun kidime ne lokacinda wasu matasa rike da wukake suka fara satar wayoyin mutane, wasu kuma sun ce rashin iya aiki ne na 'yan sanda na shawo kan taron jama'a ya haddasa turmutsutsun.

Lamarin ya faru ne kusa da babban filin wasa dake Abidjan babban birnin kasar ta Ivory Coast, bayan da aka kammala bikin da ya samu halartar dubun dubatar jama'a.

Shugaban kasar Alassane Quatarra, ya ziyarci wadanda suka samu raunuka a sibiti a birnin Abidjan, sannan ya ce gwamnati za ta dauki nauyin maganin da za a yiwa dukkan wadanda suka jikkata.

Mr Ouattara ya kuma bayyana cewar za a gudanar da bincike, tare da daukar matakan kare sake abkuwar lamarin.

Karin bayani