Amurka ta kauce wa fadawa kangin tattalin arziki

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama

Amurka ta kauce wa fadawa wani matsanancin hali na tattalin arziki, bayan majalisar wakilan kasar ta amince da yarjejeniyar da fadar White House da majalisar dattawa suka amince da ita

Ta dakatar da shirin zaftare kudaden da gwamnati ke kashewa da karuwar haraji ga 'yan kasar da daama abinda masana tattalin arziki suka ce daa yaa kai ga durkusar da tattalin arzikin kasar.

Shugaba Obama ya ce yarjejeniyar ta cika masa daya daga cikin alkawurran da ya yi, a lokacin yakin neman zabe, amma ya kara da cewa ana bukatar kara tashi tsaye wajen habaka tattalin arzikin kasar.

A wannan yarjejeniya an kara lafta wa attajiran Amurka haraji, abinda shugaban kasar ke so, akwai kuma batun rage kudaden da ake kashewa, kamar yadda 'yan jam'iyyar Republican suka nema.

Sai dai kuma ba a san ko a kan ko wane mataki hakan zai kasance ba, sai an yanke shawara nan gaba.

Tun lokacinda ake muhawara,Jagorar jam'iyyar Democrat a majalisar wakilan Nancy Pelosi - ta ce zaben Shugaban kasa ya nuna cewar Amurkawa suna son yin watsi da batun bambancin siyasa.

Masu sharhi kan al'amuran da suka shafi tattalin arziki dai sun sha gargadin cewa idan ba a gaggauta warwarewa ba, matakan ka iya sake jefa Amurka cikin kangin tattalin arzikin.