An mammana fostocin Shugaba Jonathan a kan 2015

jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

A Najeriya, al'ummar da ke Abuja, babban birnin kasar, sun shiga sabuwar shekara ta 2013 ne da wasu hotunan shugaban kasar, Dr Goodluck Jonathan, da aka mammana a tituna, na neman tsayawa takara a shekara ta 2015.

An dai lillaka hutunan ne a wasu manyan tituna da sauran wuraren taruwar jama'a.

Tuni dai wasu 'yan jam'iyyun hamayya suka fara tofa albarkacin bakinsu a kan wannan lamari, wadanda ke cewa ba sa tsoron karawa da shugaban kasar a zabe na gaba.

Da wadannan hotuna dai za a iya cewa an fara bude shekara ta dubu da goma sha uku a Najeriya da kada gangar siyasa.

Kuma wannan ya tabbatar da hasashen da wasu masana harkokin siyasa suka yi cewa watakila hankalin shugabanni a 'yan siyasa zai fara rajja'a ga yakin neman zaben shekara ta 2015 tun a farkon wannan shekara ta 2013, kuma idan haka ta kasance, to da wuya su samu natsuwar aiwatar da ayyukan raya kasa.